Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta Kaddamar da kwamiti kan rikicin Boko Haram

REUTERS/Afolabi Sotunde

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta kaddamar da kwamiti da zai duba hanyoyin magance rikicin da ake dangantawa da kungiyar Boko Haram.Kwamitin na mutun bakwai ya kunshi wasu daga cikin ministocin kasar, kuma cikekken bayani kan aiyukan da aka tsara wa kwamitin.Kwamitin da Shugaba Goodluck Jonathan ya kaddamar ana saran zai mika rohotonsa zuwa ranar 16 ga wannan wata na Agusta.