Amurka

Majalisar Amurka ta amince da kudirin dage shingen bashin da kasar zata iya ci

REUTERS

Majalisar Wakilan kasar Amurka, ta amince da kudirin dage shingen bashin da kasar zata iya ci, bayan an dauki makwanni ana ta tafka mahawara.Shugaban Majalisar, John Boehner, ya sanar da cewa, mutane 259 suka amince da kudirin, yayin da 161 suka ki amincewa da kudirin.Shugabar Yan Majalisun Jam’iyar Democrat, Nancy Pelosi, ta zargi Majalisar da jefa siyasa cikin al’amarin, wanda ya dace ace an kammalashi tuntuni.Anasa bangaren Prime Ministan Russia, Vladimir Putin, ya bayyana kasar Amurka, a matsayin wani kauci dake cin tattalin arzikin duniya, inda ya ce Dalar Amurka na barazana ga harkokin kasuwanci a duniya.Putin ya shaidawa wata kungiyar matasa cewar, Amurka na kashe kudaden da bata da su, kuma daga bisani ta dora nauyin kan tattalin arzikin duniya.