Guatemala

An Daure wasu tsaffin jami'an Sojan kasar Guatemala

Wata Kotu a kasar Guatemala, ta daure wasu Tsoffin sojin kasar hudu, shekaru 12,060 kowanne dayansu, saboda samun su da laifin yanka fararen hula 200, lokacin yakin basasan kasar, a shekarar 1982.Kotun ta ce sojin sun kwashe kwanaki uku ne suna kashe mutanen, a wani gari da ake kira Dos Erres, a karkashin jagorancin shugaban kasa Janar Efrain Rios Montt.