Somaliya

Fada na baraza wajen kai kayan agaji Somaliya

REUTERS/Feisal Omar

Yayin da ake ci gaba da yi gargadin cewa karancin abinci zai iya daidaita yankin kudancin kasar Somaliya, lamuran rarraba kayan agaji na samun tarnaki sakamakon fadace fadacen da ake yi, da kuma iyakokin da ‘yan tawayen kasar suka sa.A watan jiya ne MDD, ta ayyana afkuwar karancin abinci da za ta iya shafar kimanin mutane miliyon 12 a yankin kudacin kasar ta Somaliya, sakamakon fari da ya dade yana damun yankin.