Faransa

Faransa zata mayar da Tsohon Shugaban Panama Noriega zuwa Gida

Tsohon Shugaban Panama Manuel Noriega
Tsohon Shugaban Panama Manuel Noriega REUTERS/Alberto Lowe/Files

Kasar faransa ta tabbatar da bayar da umarnin mika tsohon shugaban kasar Panama Manuel Noriega, zuwa kasarsa, don fuskantar zarge zargen da suka hada da halarta kudaden haram da fataucin miyagun kwayoyi.Halin yanzu Noriega na zamar gidan yari a kasar ta Faransa.