Sudan

An hallaka hudu daga Dakarun MDD dake Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, dakarun ta dake aikin samar da zaman lafiya a Abyei, dake kasar Sudan guda hudu, da suka fito daga kasar Habasha, sun rasa rayukansu, bayan sun taka bam.Kakakin dakarun, ya ce wasu bakwai sun samu raunuka, a Mabok, dake kudancin Abyei.