Sudan ta Kudu

Kungiyar Yan Tawayen Sudan ta Kudu ta aiyana tsagaita wuta

© Reuters

A yau Laraba, wata kungiyar ‘yan tawayen kasar Sudan ta kudu, da ke karkashin jagorancin Janar Peter Gadet, sun amince su ajiye makamai ba tare da gindaya sharadi ba.‘Yan tawayen sun kuma amince su fara tattaunawa don rikidewa su shiga rundunar sojan kasar.Wani da ya yi jawabi a madadinsu, ya ce suna da dakaru kimanin dubu 10. Cikin watan jiya na Yuli kasar ta Sudan ta Kudu ta aiyana samun 'yanci daga cikin kasar Sudan, kamar yadda yarjejeniyar kawo karshen yakin basasa ta shekara ta 2005, ta tanada.