Italiya

PM Italiya Berlusconi ya yi jawabi kan matsalar tattalin arziki

PM Italiya Silvio Berlusconi
PM Italiya Silvio Berlusconi REUTERS/Stringer

PM kasar Italiya Silvio Berlusconi ya bayyana cewa kasar Italiya ba zata shiga matsalar tattalin arziki ba, kamar wasu kasashen Turai, saboda ingantattun ginshikan tattalin arziki da kasar ta ke kai.Ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa bankunan kasar sun tsallaka siradi game da matsalar tattalin arziki.Tunda fari, jiya Laraba Ministan kudin kasar ta Italiya Giulio Tremonti, ya yi wata tattaunawa da babban jami’i mai kula da tattalin arziki na tarayyar Turai, domin samo hanyar da za bayar da tallafi ga kasahen Italiyar da Spain.Kasar ta Italiya ita ce kasa ta uku mafi karfin tattalin arzikin a tsakanin kungiyar EU, ta nemi tallafi daga Tarayyar ta turai. Kuma tana neman kudaden da suka kai dala bilyan 43, daga tsuke bakin aljuhu.