Amurka

Shugaban Amurka Obama ya nemi bunkasa tattalin arziki

Shugaban Kasar Amurka Barack Obama
Shugaban Kasar Amurka Barack Obama Reuters

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama, ya sanya hannu kan dokar da 'yan Majalisun kasar suka amince da ita, na kara yawan bashin da kasar zata iya ci, na Dala triliyon kusan biyu da rabi.Shugaba Obama ya yi kira ga majalisar kasar ta mayar da hankali kan bunkasa tattalin arzikin kasar da ke cikin wani mayuyacin hali.Cikin jawabin da ya yi wa jama’ar kasar daga lambun Rose Garden, shugaban ya ce bai kamata a sake dora dawainiyar kasafin kudin kasa kan jama’ar da suka riga suka yi fama da matsalar tabarbarewar tattalin arzikin kasa ba.Ya ce kowa na da rawar da zai taka, inda ya ce kamata ya yi ‘yan majalisa su mayar da hankali kan dokokin da ke yin ta’annati ga ci gaban kananan kanfanoni, da kuma sa manyan kamfanoni masu zaman kansu, su farfado da ababen more rayuwa.Shugaba Obama ya kuma sha alwashin kokarin ganin an samar da ayyukan yi, Karin albashi da ci gaban tattalin arzikin kasa, lamuran da Amurkawa da dama ke fatar gani.