Nijar

Shugaban Janhuriyar Niger ya tabbatar da yunkurin juyin mulki

Shugaban kasar janhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou
Shugaban kasar janhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou ©RFI/Delphine Michaud

Shugaban Janhuriyar Niger, Mahammadou Issoufou, ya sanar da kama mutane 10, da ake zargi da kitsa aiwatar da juyin mulki ranar 12 da 13 ga watan da ya gabata, na Yuli.Wata sanarwa da shugaban ya bayar ta kafar talabijin, yac e daya daga cikin wadanda ake zargin ya tsere. Shugaban ya yi jawabin albarkacin cika kasar ta Janhuriyar Niger shekaru 51 da samun 'yanci daga Turawan mulkin mallakan kasar Faransa.