MAsar

Tsohon Shugaban Masar Mubarak ya Musanta zargin da ake ma shi

Tsohon shugaban kasar Masar Hosni Moubarak
Tsohon shugaban kasar Masar Hosni Moubarak REUTERS/Egypt TV via Reuters

Tsohon Shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak, yaki amincewa da tuhumar da ake masa na cin hanci, da kuma kashe masu zanga zanga. Yayin da ya gurfana a gaban kotu, Tsohon shugaban wanda aka kai kotun a gadon asibiti, yace shi bai aikata laifi ba.An kai Mubarak kotun kan keken tura marasa lafiya, kuma yana sanye da fararen kaya.Ana cajin tsohon Shugaban da laifukan almundahana da dukiyar al’uma, da kisan masu zanga zanga kafin kawo karshen gwamnatinsa.Mubarak yana fuskantar shariyar tare da ‘ya’yansa Alaa da Gamal, da wasu tsaffin jami’an gwamnatinsa da suka daha da tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida Habib al-Adly.An girke kimanin jami’an tsaro 3,000 a wajen kotun dake Alkahira babban birnin kasar ta Masar.