Lafiya Jari ce

Bada Jini A Matsayin Taimako

Sauti 10:00

Alkalumma daga hukumar lafiya ta duniya WHO, na nuna cewa karancin jini ko bukatar sa cikin gaugawa, na cikin dalilan dake kan gaba wajen halaka mata masu juna biyu da kananan yara a kasashe masu tasowa. Wannan hadi da cututtukkan dake haddasa karancin jini a jikin Dan Adam musamman Anemia da Zazzabin cizon sauro na Malaria, hadurran mota da rikice-rikice inji hukumar ta WHO, yasa bukatar jini da kuma tara shi cikin mayan batutuwa na kiwon lafiya a wannan karnin. Sai dai kuma duk da wannan muhimmancin na jini a jikin Dan Adam yawancin jama'a na nokewa da yin dari-darin bada jini a matsayin taimako. Wannan kuwa na faruwa ne, duk cewa a kimiyyace babu wata illar yin haka.Kamar yadda bincike ya nuna, fargaba,jahilci da wani zibin talauci, sune kan gaba wajen nisanta mutane daga wannan batu na bada jini a matsayin taimako. Shirin Lafiya Jari na wannan makon ya duba muhimmancin wannan batu na bada jini,fargabar da wasu ke bayyanawa kan wannan al'amari da kuma yadda watakila za'a sake farfado da kishin bada jini domin ceto al'umma daga babban kalubale na rayuwa.