Ilimi Hasken Rayuwa

Google+: Dandalin Zumunta

Sauti 10:00

A kwanan ne kamfanin Google ya kaddamar da wani sabon shafin dandalin zumunta a internet wanda zai yi gogayya da dandalaye irinsu Facebook da Twitter wadanda suka shahara. Akwai dai abubuwa da dama da kamfanin na Google yake ganin rauni ne a sauran dandalayen, kuma haka ne ya sanya kamfanin ke tunanin samar da wasu sabbin sauye sauye a tsarin dandalin zumunta sabanin sauran dandalen da ke bai wa mutum damar mallakar abokanai ba tare da wani shamaki ba.Shirin “Ilimi Hasken Rayuwa” ya tattauna da masana fasahar sadarwa dangane da kaddamar da sabuwar fasahar dandalin zumunta na Google+. Ko yaya za’a danganta shi da sauran dandalayen kamar Facebook wanda ya samu karbuwa a duniya baki daya.