Lafiya Jari ce

Tsarin Bada Agaji Na Gaugawa

Sauti 10:00

Agajin gaugawa shine taimakon da akan ba mutanen da hatsari,annoba ko wani bala'i ya ritsa dasu. A nan ana magana wani dan kankanin lokaci watau tsakanin faruwar wannan hatsarin ya zuwa lokacin da za'a isa asibiti ko kuma samun wani kwararren da zai taimaka.Alkalumma daga hukumar lafiya ta duniya WHO,na nuna cewa samun ingantaccen tsarin bada agajin na gaugawa musamman wanda kasa da kasa suka amince dashi,na iya rage asarar rayukka daga hatsari ko wani bala'i da akalla kashi 60 cikin 100.Sai dai kuma sabanin abinda ke faruwa a kasashen Turai da Amurka inda ake bin tsarin kai daukin gaugawa sau-da-kafa,a Nigeria kamar sauran kasashe masu tasowa,ana cigaba da fuskantar matsaloli na karancin kayan aiki da ingantaccen tsarin tunkarar hatsari ko wata annoba.Shirin Lafiya Jari na wannan makon,ya duba yadda tsarin bada agaji na gaugawa ke gudana a Nigeria,matsalolin da ake fuskanta wajen cheton rayukka a yayin wani hatsari ko annoba da kuma yadda watakila za'a kyautata wannan tsarin.