Najeriya

Hamza al-Mustapha ya bada shaida mai daukan hankali a kotu

Major Hamza al-Mustapha
Major Hamza al-Mustapha

‘Yan Nigewria na ci gaba da sauraron kafofin yada labarai sau da kafa domin bi dalla-dalla fasa kwai da Hamza Al-Mustapha, Dogarin Tsohon Shugaba Marigayi Janar Sani Abacha, ke ta yi a babbar Kotun Lagos.A jiya Alhamis, Kotun ta kalli wani hoton Video ne da Hamza al-Mustapha ya gabatar dake nuna wasu fitattun Shugabannin Yarabawa 2 nata farin ciki bayan sun gana da tsohon Shugaban Nigeria Janar Abdulsalam Abubakar Mai murabus.A zaman na jiya dai Hamza Al-Mustapha ya shigar dasu Nuhu Ribadu, da tsohon Shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo da Abdulsalam Abubakar wadanda duka sun nemi a hallaka shi gudun kada yayi irin wadannan tonon sililin.Manjor Hamza Al-mustapha da azumi a bakinsa kuma sai da ya saba Alkurani mai girma kafin ya fara tonon sililin.