Libya

Harin dakarun NATO ya hallaka mutane 30 a kasar Libya

REUTERS/Ismail Zetouny

A rikicin kasar Libya wani hari da dakarun NATO suka kai a yammacin zliten ya yi sanadiyar mutuwar mutane 30 kuma ana tunanin cikin su har da Khamis dan dan shugaba Muammar Gaddafi.A cewar Al Zawawi kakakin ‘yan tawayen na Libya, NATO ta kai harin ne a wani gidan da dakarun Gaddafi ke fakewa a birnin Zliten.Khamis dai na daya daga cikin manyan kwamandojin dakarun Mu’ammar Gaddafi da ke bada umurnin yaki a Zliten.Sai dai kuma gwmnatin kasar ta Libya ta musanta mutuwar Khamis dan na Mua’ammar Ghaddafi.