Faransa

Kotun kasar Faransa zata binciki Shugabar IMF Lagard

Christine Lagarde Shugabar Hukumar IMF ko FMI
Christine Lagarde Shugabar Hukumar IMF ko FMI REUTERS/Kevin Lamarque

Wata kotun kasar Faransa ta bayar da umarnin gudanar da binciken kan shugabar Hukumar Lamani ta Duniya, IMF, Christine Lagarde, saboda zargin aikata ba daidai ba a lokacin da take rike da mukamin Ministan kudin kasar Faransa.Alkalan kotun kasar sun bayyana shawarar da suka dauka ta kafa kwamitin binciken da zai duba lamarin, kamar yadda babban Alkali ya bayyana.Christine Lagarde, da ta fara aiki a matsayin Shugabar hukumar ta IMF a watan da ya wuce, ta ki amincewa ta saba ka’ida a lamarin da ya shafi biyan wani dan kasawa mai zaman kansa kudade daga aljihun Gwamanti, a shekara ta 2008 lakacin da take ministan kudin Faransa.Sai dai kuma ‘ya ‘yan kwamitin gudawarar IMF, sun bayyana goyon bayan su ga Mrs. Lagarde, da ta gaji Dominique Strauss Khan, da aka zarga da yunkurin yi wa wata mace fyade.Irin wannan bincike zai iya sanadin gurfanar da Lagarde, kuma in har aka same ta da laifi, zata iya zuwa gidan yari na shekaru 10, da tarar da ta kai EURO 150,000.