Somaliya

Mutane biyar sun hallaka cikin farmakin Somaliya

AFP PHOTO/MUSTAFA ABDI

Akalla mutane sun hallaka cikin farmakin da ‘yan bindiga dadi na kasar Somaliya suka kai Mogadishu babban birnin kasar.Yan bidigan sun sace kayan abinci agaji dake wannan sansani na ‘yan gudun hijira, wanda aka kai domin raba wa dubban mutanen dake fuskantar barazanar yunwa.Wani jami’in bada agaji na kasar ta Somaliya ya bayyana cewa akwai kimanin ton 300 na kayan abinci, wanda Hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta kawo, yayin da barayin suka kai hari.