Ukrain

PM Ukrain Azarov ya bada shaida kan shariyar Tymoshenko

PM Ukraine Mikola Azarov da Shugaban kasar Viktor Ianoukovitch
PM Ukraine Mikola Azarov da Shugaban kasar Viktor Ianoukovitch Konstantin Chernichkin/Reuters

A yau jumma’a kuma Prime Ministan Ukrain Mykola Azarov, ya kai wata ziyarar bazata a kotu a mastayin shaida, a ci gba da sauraren wadda ya gada Yulia Tymoshenko.Ana dai zargin Tymoshenko ne da laifin yin amfani da mukaminta ta hanyar da bata dace ba wajen kulla wata yarjejeniyar iskar Gas da kasar Rassia a shekarar 2009.Al’amarin da ke neman haramta mata shiga harakokin siyasar kasar tare da daurin shekaru 10 a gidan yari.