Faransa

Yan Siyasan kasar Faransa na hutu a gida

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy
Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy Reuters/E.Vidal

Dimbin ‘yan siyasar kasar Faransa na hutun da aka saba na wannan lokaci a gidajensu, maimakon yawon bude idanu a kasashen duniya da aka saba.Hutu a irin wannan lokaci a kasar ta Faransa da sauran kasashen Tura dai ba'a barin kowa a baya, kama daga yaran makaranta, kantunan saida-sayarwa, ma'aikata dama gidajen jaridu kan tafi hutun da aka saba na akalla makonni uku, tsakanin watan jiya na Yuli da wannan watan na Agusta.Tun a watan jiya Shugaba Nicolas Sarkozy ya ja kunnen Ministoci da cewa Ministan baya hutu, alamarin dake sa masu lura da alamurran yau da kullun ke ganin matakan da Hukumomin kasar ke dauka baya rasa nasaba da tsumin kudade, ga shirin babban zabe dake tafe da dai fargaban kada a sake yin tabargazar da akayi a baya na wasu kusoshin Gwamnati dakan yi amfani da lokuttan hutun nasu a tafi maula wasu kasashe.