Us-Afghanistan

Sojan Amirka 30 Sun Mutu A Kasar Afghanistan

Daya daga cikin jiragen Amirka da ya fadi a kasar Afghanistan
Daya daga cikin jiragen Amirka da ya fadi a kasar Afghanistan RFI

Sojan kasar Amirka 30 ne dake aiki a kasar Afghanistan, suka rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin jirgin saman su mai saukan ungulu.Wadannan sojoji dai kwararru ne matuka da ake ji da su, domin sune ma suka bi dare suka kashe madugun kungiyar Alkaida Osama Bin Laden.Wannan rashi ya kasance mafi muni, tashi guda, ga kasar Amirka tun fara yakin da take yi a kasar Afghanistan. Kungiyar Taliban tace aikinta ne kakkabo jirgin.Kasar Amirka na binciken wannan ikirari.