Turai

Ana ci gaba da samun matsaloli game da tattalin arzikin manyan kasashen Duniya

AFP PHOTO/ JAVIER SORIANO

Fargabar yadda zata kasance wayewar gari yau Litinin game da faduwar kasuwannin hannun jari a Turai, tasa masu ruwa da tsaki game da kudade a kasashen Turai hana idanunsu barci, kafin bude kasuwar ta yau Litinin.Jiga-jigan jami'ai daga kasashen Duniya da masana da kwararru, da Gwamnonin Manyan Bankunan Turai sun yi ta taruka daban-daban jiya Lahadi, da niyyar tunkarar babbar matsalar data kunno kai makon jiya.Ministocin Kudade da Shugabannin Manyan Bankunan Kasashe masu karfin tattalin Arziki na kasashen kungiyar G7, Birtaniya, Canada, Faransa, Jamus, Italiya, Japan da Amurka sun yi nasu tarukan ne ta wayoyin tarho domin fito da matsaya.A wata alama dake nuna lamarin na iya munana wannan makon, kasuwar hannun jari na Isra'ila ya dan ja baya jiya Lahadi, yayind a kasuwannin kasashen Gabas ta Tsakiya ma basu tsira ba.Wannan matsalar faduwar hannun jari da ta haifar da fargabar gaske gudun kada a fuskanci matsalar tattalin arzikin a fadin duniya.Da yammacin jiya kungiyar dake auna kasashe da ake kira Standards and Poor ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar kara lalacewar harkan basussukan kudade a kasar Amurka.