Najeriya

Babban Bankin Nigeria ya karbe Bankuna uku

路透社

Hukumar Dake kula da saida hannayen jari ta Tarayyar Nigeria, ta dakatar da hada hadan hannayen jarin bankuna uku da Babban bankin kasar ya karbe, wato Afribank, Spring Bank da Bank PHB.Babban Bankin na Nigeria, a karo na biyu, ya karbe ragamar tafi da Bankunan kasar uku dake fuskantar matsaloli, abinda ya jefa masu ajiya a wadanna bankuna cikin fargaba da rudani.