Somaliya

Dakarun Somaliya sun kwace yankunan birnin Magadishu

AFP/Mustafa Abdi

Dakarun Gwamnatin Somalia, dake samun goyan bayan dakarun kungiyar kasahsen Afrika ta AU, sun kwace wasu Yankunan dake karkashin kungiyar Al Shabaab.A wani labarin, Hukumar Jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce yau Litinin zata jigilar kayayakin da aka fi bukata Mogadishu, a ci gaba da kai agaji da take yi kasar, dake fama da matsalar yunwa.Wakilin hukumar a Nairobi babban birnin kasar Kenya, Brino Gedo, ya ce jirgi mai dauke da kayan agaji 2,500 zai sauka a Mogadishu da misalin karfe 11 agogon kasar.