Faransa

Faransa da Jamus sun nemi aiwatar da yarjejeniyar ceto kudin Euro

Shugaba Sarkozy na Faransa da Uwargida Angela Merkel na Jamus
Shugaba Sarkozy na Faransa da Uwargida Angela Merkel na Jamus REUTERS

Kasashen Faransa da Jamus, sun bukaci aiwatar da yarjejeniyar da suka amince da ita, a watan Yuli, dan magance kasuwannin kasashen dake anfani da kudin Euro.A tattaunawar da suka yi, Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa da Angela Merkel ta Jamus, duk sun sake bayyana cikaken goyan bayan su na aiwatar da daukacin shirin, da shugabanin kasashen Turai suka dauka, ranar 21 ga watan Yuli.