Sudan

Jami'an Tsaro a Sudan sun kwace daukacin Jaridar Al Ahdat da aka buga jiya Lahadi

Jami'an Tsaro a Sudan, sun kwace daukacin Jaridar Al Ahdat, da aka buga jiya Lahadi, a wani yanayi da ake ganin na musgunawa kafofin yada labarai ne.Editan Jaridar, Adil al-Baz, ya ce an kwace jaridun ne, saboda rahotan da suka buga kan Jam’iyar SPLM ta Sudan ta kudu, da kuma cin hanci da aiyukan ta’addanci.Ya zuwa yanzu dai hukumomin basu ce komai ba.