Amurka

Sakataren Baitulmalin Amurka Geithner zai ci gaba da rike mukamun

Sakataren Baitulmalin Amurka Timothy Geithner
Sakataren Baitulmalin Amurka Timothy Geithner Reuters/Jason Reed

Baitulmalin Amurka, ta sanar da cewa, Sakataren ta, Timothy Geithner, ba zai sauka daga mukamin sa, duk da kirayen kirayen da 'yan Jam’iyar Republican ke masa, saboda rage darajar tattalin arzikin kasar.Kakakin Baitulmalin, Jenni Lecompte, ta ce Geithner ya shaidawa shugaba Barack Obama cewar, zai ci gaba da zama a kujerarsa, dan magance matsalar da ake fuskanta yanzu haka.