Venezuela

Shugaban Venezuela Chavez zai koma kasar Cuba jinya

Shugaban Kasar Venezuela Hugo Chavez
Shugaban Kasar Venezuela Hugo Chavez ©Reuters.

Shugaban Kasar Venezuela, Hugo Chavez, ya isa kasar Cuba, dan ci gaba da samun maganin sankarar dake damun sa.Shugaban mai shekaru 57, wanda tuni cutar ta sanya zubewar gashin kansa, ya bayyana fatar sa na komawa Venezuela cikin 'yan kwanaki masu zuwa.