Libya

Yan Tawayen kasar Libya sun kama gari kusa da Tripoli

Garin Bir Ghanam
Garin Bir Ghanam Reuters/Bob Strong

Yan tawayen kasar Libya sun kama garin Bir al-Ghanam mai nisan kilo mita 80, kudancin Tripoli babban birnin kasar.Dan jaridar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, wanda yake birnin ya tabbatar da labarin, saboda rashin kara kainar dakarun gwamnatin cikin garin, kuma ya bada labarin ganin konannun tankokin yaki uku, da makaman atilari na soja da aka tafia ka bari.