Lafiya Jari ce

Mata Masu Ciki Da SIDA

Sauti 10:20
RFI Hausa

Kamar yadda aka sani dai cutar SIDA, cuta ce mai karya garkuwar jiki kuma cuta ce da ke ci gaba da yaduwa tsakanin matasa maza da mafi yawan yara yaran mata. Cuta ce da wasu ma'aurata suka tsinci kansu da ita suka kuma amince da su ci gaba da rayuwar aurensu tare. To ko tana yiwuwa macce mai cutar SIDA ta samu juna biyu wato ciki ba tare da ta saka wa jaririnta ba ? Tambayar da likitoci suka amsa a cikin wannan shirin da cewa tana yiwuwa idan har maccen ta bi shawarar likitoci a cikin tsarin PTME tsarin nan na binciken harakar SIDA da kare da uwa. Na kuma samu macen da ta shaida da bakinta cewa a wurin awon ciki aka gane tana da cutar ta bi tsarin kuma ta haifi danta lafiya.