Libiya

"Yan Tawayen Libiya Na Samun Nasara

Yanayin barin wuta da ake yi a Libya
Yanayin barin wuta da ake yi a Libya RFI

‘Yan tawayen kasar Libya, dake hakilon kifar da Gwamnatin Shugaba Moammar Gaddafi, na rike da garin Tuarga tun ajiya, inda ake ganin ba karamar nasara ce ba kama wannan muhimmin gari, a kwana na uku da suke fafatawa don Koran Dakarun Gwamnati.Bayanai na nuna cewa tun Juma'a ‘Yan tawayen ke ta fafatawa da Dakarun Gwamnati dakan makale a wasu mabuya suna tsinci daidai.Kwace garin ana ganin nasara ce babba ga ‘yan tawayen domin zasu kori Dakarun Gaddafi daga yankin Misrata. A halinda ake ciki mai Magana da yawun Gwamnatin Gaddafi Mousa Ibrahim yace ikirarin kama wani gari, musamman gari Zawiyah da ‘yan tawayen ke murna karya ne.