Britaniya

Za'a Sanya Kafar Wando Daya Da Masu Bore A Britaniya

Daya daga cikin wadanda ake zargi wajen boren kasar Britaniya
Daya daga cikin wadanda ake zargi wajen boren kasar Britaniya RFI

Fira Ministan kasar Britaniya David Cameron yace Hukumomin kasar zasu sanya kafar wando daya da masu bore,  da suka yi ta yi dan tsakanin nan har da kwasan ganima.A yanzu haka dai yau lahadi biyu daga cikin wadanda aka kama zasu gurfana gaban kotu saboda sanadin mutuwar mutane 3.Fira Ministan yayi hayan wani tsohon Jami'in ‘Yan sandan New York ne, mai suna Bill Braton domin bashi shawaran yadda zasu tunkari lamarin.A halin da ake ciki kuma Hukumomin kasar Britaniya sunce za'a cigaba da gudanar da sauye-sauye a Hukumar 'Yan sandan kasar da zai kaiga rage yawan 'Yan sanda, duk da matsalolin dake kunno kai dake bukatar su.Ministan kudade George Osborne ya fadi cewa shi kansa da Fira Ministan kasar da kuma Sakataren Harkokin Cikin gida na shaawan ganin an gudanar da sauye-sauyen.