Syria

Babu Sauran Kashe Masu Bore- Inji Shugaba Al-Asad Na Syria

Shugaban Syria Bashar al Assad
Shugaban Syria Bashar al Assad Rfi

Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya bayyana katse duk aiyukan soja kan masu zanga zangar neman ya yi murabus daga kan madafun iko.Ya bayyana haka wa babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon cikin tattaunawa ta wayar tarho.Masu rajin kare hakkin bil Adama sun bada labarin cewa dakarun kasar ta Siriya, na tsare da daruruwan masu zanga zanga a filin wasa na garin Latakia mai tashar jiragen ruwa.