Isra'ila

Hamas Ta Musanta Hannu Wajen Harin Yau A Israela

Sojan Israela na tsaye kusa da mota da aka kaiwa hari
Sojan Israela na tsaye kusa da mota da aka kaiwa hari Rfi

Kungiyar Hamas ta musanta hannu wajen harin da ya kashe mutane akalla bakwai a kudancin Israela yau.Ministan Tsaro na kasar Israela Ehud Barak tunda fari ya fadi cewa maharan daga zirin Gaza suka fito inda kungiyar Islama ta Palestinawa ke rike dashi.Mai magana da yawun Hamas Taher al-Nunu ya fadawa kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP cewa wannan hari, dabara ce, ana neman kawar da hankalin bore ne gameda hauhawan farashin rayuwa a Israela.