Spain

An Kama Wani Matashi Da Kai Hari Kan Masu Bore Da Ziyarar Paparoma a Spain

Paparoma Benedict da isowarsa Spain.
Paparoma Benedict da isowarsa Spain. RFI

Wani dalibi dan kasar Mexico Jose Alvano Perez Bautista ya gurfana gaban kotu yau saboda zargin da ake yi masa na hannu wajen kai hari da guba kan masu bore da ziyarar Paparoma Benedict XVI a kasar Spain.Masu boren na nuna hushinsu ne da yadda za'ayi amfani da kudaden Gwamnati wajen yiwa Paparoma karba ta alfarma.Matashin dalibin mai shekaru 24 na daga cikin mutane 30,000 da akayi hayansu domin taimakawa bukin marhabin da Paparoma a kasar Spain tsakanin 16 zuwa 21 na wannan watan.'Yan Sanda sun kwace naura mai kwakwalwa, littafai da wasu kayan matashin.