Syria

Gwamnatin Bashar al-Asad Na Syria Yau Sun Kashe Mutane 19

Wasu mamata da kungiyar Amnesty ke zargi Gwamnatin Bashar al-Asad sun kashe
Wasu mamata da kungiyar Amnesty ke zargi Gwamnatin Bashar al-Asad sun kashe RFI

Dakarun Syria sun kashe masu bore akalla 19 yau Juma'a, kwana daya bayan Shugaban kasar Bashar al-Asad ya furta cewa babu sauran kashe masu bore a fadin kasar.A halin da ake ciki kasar Russia da kasar Turkiyya sun furta kin amincewa da raayin Shugaban kasar Amirka Barak Obama dake neman kasashen duniya daa tursasawa Shugaban Syria da yayi bankwana da mulkin kasar.Wani Jami’in kungiyar kasashen Turai yace za'a cigaba da malkayawa kasar Syria takunkumi wajen harkar Mai.