Afghanistan

An Kai Hari Ofishin Al'adun Britaniya Dake Kabul

Daya daga cikin wadanda suka sami rauni an kwashe shi zuwa asibiti na Kabul
Daya daga cikin wadanda suka sami rauni an kwashe shi zuwa asibiti na Kabul RFI

Mutane 8 ne suka rasa rayukansu a wani hari ofishin Britaniya dake Kabul na kasar Afghanistan kuma har Kungiyar Taliban ta amsa cewa aikinta ne wannan hari.Yau Juma'a ranar hutu ne domin girmama ranar da aka kawo karshen yakin shekara ta 1919.Wani mai magana da yawun ‘yan tawaye ya fadi cewa harda wani gidan baki na Majalisar Dinkin Duniya da aka kai hari, amma kuma Majalisar ta musanta haka.Ofisoshin kasar Britaniya dake Kabul kan kasance karkashin jami'an tsaro na kamfanoni masu zaman kansu ne.A fafatawan da akayi yau, dakarun kasar Afghanistan, Britaniya, Faransa da na Amirka sun taimaka domin fatattakan maharan.Cikin mamatan akwai ‘yan sanda biyu da wasu masu aikin shara.