Egypt-Israel

Masar Ta Janye Jakadan Ta Daga Israela

Masu boren hari da Israila ta kaiwa Masar
Masu boren hari da Israila ta kaiwa Masar RFI

Kasar Masar ta janye jakadan ta dake kasar Israela domin nuna rashin jin dadin ta da kisan wasu ‘yan sandan ta biyar da akayi a kan iyaka, wajen neman ramuwar hari kan Palestinawa.Hafsan Hafsoshin Sojan kasar Masar Sami Enan tun ajiya ya jagoranci wata tawaga domin binciken lamarin.Bayanai na cewa kasar Masar na bukatar neman gafara daga kasar Israela gameda abinda ya faru.