Malawi

Shugaban Malawi Ya Rusa Majalisar Zartaswan Kasar

Shugaba Bingu wa Mutharika na kasar Malawi
Shugaba Bingu wa Mutharika na kasar Malawi RFI

Shugaban kasar Malawi Bingu Wa Mutharika wanda yake fuskantar tsinewa daga jama'an kasar saboda salon mulkin sa ya rusa majalisar zartaswan sa.Babu wasu dalilai daya gabatar saboda daukan wannan mataki.Babu kuma takamaiman lokacin da yace zai nada sabuwar majalisar zartaswan kasar.Masana na ganin Shugaban ya tara cima zaune ne cikin majalisar zartaswan kasar, al'amarin dake janyo masa Allah wadai.