Libya

Kazamin Fada Ya Rinchabe A Birnin Tripoli Na Libya

Shugaban Libya Moammar Gaddafi cikin tunani
Shugaban Libya Moammar Gaddafi cikin tunani RFI

Shugaban kasar Libya Moammar Gaddafi cikin wani jawabi dazun nan ya bukaci Dakarun sa da kada su bada gari, su gwabza fada sosai domin kwace duk inda 'yantawaye ke cewa sun kwace.Shugaba Gaddafi ya kira masu yakar sa beraye da azzalumai.'Yan tawayen kasar Libya sunce hakjarsu saura kiris ta cimma ruwa, tinjim, domin kuwa sun dira a  Babban birnin kasar Tripoli.‘Yan tawayen sun fadi cewa karshen mulkin shekaru 42 na Moammar Gaddafi yazo karshe.Bayanai na cewa anyi ta jin karar manyan harsasai ba kakkautawa, a birnin Tripoli, kuma akwai rahotannin fada a wasu garuruwa dake kusa.Mai Magana da yawun Gwamnatin kasar Moussa Ibrahim ya fadi cewa Gaddafi na rike da kasar, to amma kuma bangaren ‘yan tawayen na ta  ruguntsumin sune ke da nasara.Dan Shugaba Gaddafi Seif al-Islam wanda ya jagoranci ayarin wasu gogaggun Sojan kasar yayi jawabi dazun nan inda yake fadin babu guda ba tsoro sai sunga abin da ya turewa buzu nadi.