France-US

Mace Dake Zargin Strauss-Kahn Zata Gana Da Masu Gabatar Da Kara

Hoton Nafisatu Diallo dake zargin Dominik Strauss-Kahn
Hoton Nafisatu Diallo dake zargin Dominik Strauss-Kahn RFI

Maccen nan wadda ta zargi tsohon Shugaban Asusun Bada Lamuni na Duniya Dominik Strauss-Kahn da neman yin lalata da ita, wanda har ya kai ga saukansa daga mukamin, an bukace ta data gana da masu shigar da kara.Daya daga cikin lauyoyin nata Douglas Wigdor ya gaskata cewa gobe littini ne zaa gana da ita.Maccen mai suna Nafisatu Diallo ta lashi takobin ganin sai an daure Dominik Strauss-Kahn saboda abin tsiya da yayi mata, koda shike yayi ta musantawa.Babu dai bayani gameda dalilan gayyatan maccen, koda shike akwai wasu bayanai dake zato wata kila ayi watsi da zancen baki dayansa.