Sudan ta Kudu

Fada ya hallaka mutane 58 cikin kasar Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce akalla mutane 58 suka rasa rayukansu, a wani fadar kablianci, da ya shafi satar shanu a kasar Sudan ta Kudu.Kakakin Majalisar a Juba babban birnin kasar, ya ce an samu barkewar fadan ne ranar Alhamis, tsakanin kabilar Murle da Lou Nuer, abin da ke ci gaba da haifar da rashin kwanciyar hankali a wannan sabuwar kasa.