Najeriya

Shugaban Jonathan na Nageria ya amince da maye gurbin shugaban kotun daukaka kara Ayo Salami

Shugaban kasar Tarrayar Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban kasar Tarrayar Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, ya aiwatar da shawarar Hukumar dake kula da aiyukan shari’a, ta bashi, na sauke shugaban kotun daukaka kara, Mai-Shari’a Ayo Isa Salami daga kujerarsa, inda ya nada Mai-Shariya Dalhatu Adamu, ya maye gurbin sa.Yayin da a bangare daya kuma, kungiyar lauyoyin kasar ta ja daga dan adawa da matakin, inda take cewa tunda batun na kotu, bai dace a dauki mataki akai ba.