Libya

Yan Tawayen Libya sun samu nasarar Shiga birnin Tripoli

Reuters

Yan Tawayen Libya, sun yi nasarar shiga Tripoli babban birnin kasar, da taimakon kungiyar kawancen tsaro ta NATO ko OTAN, bayan an kwashe watanni shida ana tafka rikici a kasar.Rahotanni sun ce, 'yan tawayen sun yi nasarar kama Dan shugaba Muammar Gaddafi, Saif al Islam, yayin da na biyun ya mika kansa, amma har ya zuwa yanzu ba’aji duriyar inda shugaba Gaddafi yake ba.Shugabannin Kasashen Amurka da Faransa, Barack Obama da Nicolas Sarkozy, sun bukaci Yan Tawayen Libya, da su mutunta hakkin Bil Adama, da kuma maida kasar tafarkin demokradiya.Yayin da suke tsokaci kan halin da kasar ta samu kanta, shugabannin sun sake bayyana amincewarsu da shugabancin Yan Tawayen.