Amurka-Faransa

Kotun Amurka ta yi watsi da zargin fyade da aka yi wa Strauss-Kahn

Tsohon Shugaban Asusun Bada lamuni Dominique Strauss-Kahn
Tsohon Shugaban Asusun Bada lamuni Dominique Strauss-Kahn REUTERS/Lucas Jackson

Kotun dake sauraron zargin da ake wa Tsohon shugaban Hukumar Bada Lamini ta Duniya, IMF, Dominique Strauss Kahn, ta yi watsi da karar, abinda ya kawo karshen dambarwar da aka kwashe watanni uku anayi.Tuni dai Strauss Khan ya ce, ya zaku ya koma gida Faransa, bayan kamala wasu aiyuka a Amurka. Cikin watan Mayu aka zargi Staruss-Kahn dan shekaru 62 da haihuwa da zargin neman fyade wa Nafissatou Diallo 'yar shekaru 32, mai aiki a wani otel dake birnin New York na kasar ta Amurka.