Libya

An saka kudin lada wa duk wanda ya kamo Gaddafi amuce ko araye

Shugaban Libya Moammar Gaddafi cikin tunani
Shugaban Libya Moammar Gaddafi cikin tunani

Majalisar Rikon kwaryar ta kasar Libya, ta bayyana ahuwa wa duk wanda ya kama ko kuma ya hallaka Shugaba Muammar Gaddafi, daga cikin wadanda ke tare da shi.Shugaban majalisar Mustafa Abdel Jalil ya fadi haka, kuma yak ara da cewa akwai daya daga cikin masu arzikin garin Benghazi, da ya yi alkawarin bada lada na kudaden da suka kai milyan biyu na dinar na kasar (Euro milyan 1.2).Abdel Jalil ya bayyana haka yayin taron manema labarai a birnin Benghazi cibiyar ‘yan tawayen da taimakon kungiyar tsaro ta NATO masu ruwar wuta ta sama, suka fatattaki Shugaba Muammar Gaddafi daga fadarsa dake Tripoli babban birnin kasar.