Sharhin Jaridu

Sharhin Jaridun yau Laraba

Reuters

Zamu fara ne da jaridar Nord Eclair ta kasar Faransa wacce ta bayyana cewa Nafisatu Diallo ta fadi, duk kuwa da matsayinta, a yayin da shi kuma Dominique Strauss-Kahn da ya dage kai da fata duk kuwa da rashin ko kuma gaskiya da yake da ita, ya yi nasara, a shara’ar zargin fyade, amma kuma jaridar ta ce martabar kotu a kasar Amurka ta yi rauni.Sai kuma jaridar Le Pays ta kasar Burkina Faso wacce ta ce, Nafisatu Diallo ta fadi ne sanadiyar shirmen da ta yi, ta kwabawa ne, na magana da warwarewa, wadanda aka yi ta ji a cikin bahassan da ta bayyana, a lokutan shara’ar.Sai kuma a kasar Libiya inda akasarin jaridun Nahiyar Afrika, kamar jaridar l’Intelligent ta kasar Cote d'Ivoire, ta daura kalmar tambayar inda jagoran juyin juya halin kasar Libiya Mu’ammar Gaddafi ya ke yanzu, bayan kama birnin Tripoli da 'yan tawayen Majalisar Rikon Kwarya suka yi?Tambayar ta tsaya ba amsa, har yanzu dai makusantan Shugaban Jamhuriyar ta Libiya, da dansa Seif al-Islam da aka bayyana cewa suna cikin dakin karkashin kasa, kafin farma birnin, ba a sani ba a halin yanzu, sun jikkata ne, ko an kashe su, ba a sani ba.Sai kuma mu leka a jamhuriyar Niger inda jaridar L’Arbre a Palabres, ma’ana Itaciyar mahawara, ta bayyana cewa, gwamnatin kasar na shirin shigar da wata bukata a gaban majalisar dokoki, ta son tubewa Hamshakin dan kasuwar nan, haka kuma dan majalisar dokoki Zaku Jibbo, da aka fi sani da suna Zakai rigar kariya, domin ya gurfana a gaban shara’a badakalar kwangilar gwamnati ta Bogi, ta sama da sefa miliyan dubu biyu da a ka yi lokacin mulkin rikon kwaryar janar Salu Jibbo.Mai shigar da karar Gwamnati ya rubuta wasika zuwa ga ministan shara’a, ya na neman bukatar cirewa dan majalisar Rigar kariyar da yake da ita, a yayinda shi kuma ministan shara’ar ya gabatar da wannan bukata ga zaman taron majalisar ministocin kasar.in ji jaridarSai kuma a Nigeriya inda jaridar Daily Trust ta bayyana cewa, akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a yayinda wasu da dama suka rasa mahallansu, sakamakon ambaliyar ruwan sama da aka shatata a jiya Talata a garin Numan na Jahar Adamawa,Rahotannin sun bayyana cewa, ruwan da aka fara tun karfe biyu daren kawo wayewar safiyar yau Laraba, sun haddasa rugujewar gidajen jama’a da dama.