Sudan

Shugaban Sudan al-Bashir, ya sanar da tsagaita wuta na makwanni biyu a Jihar Kordafan

Shugaban Sudan Omar al-Bashir
Shugaban Sudan Omar al-Bashir Reuters/Mohamed Nureldin Abdallah

Shugaban Kasar Sudan, Umar Hassan al Bashir, ya sanar da tsagaita wuta na makwanni biyu a Jihar Kordafan mai arzikin mai, bayan an kawshe makwanni biyu ana ta dauki ba dadi, tsakanin dakarun sa da Yan Tawaye.Shugaba Bashir ya sanar da haka ne, yayin da ya kai wata ziyarar bazata, wanda ita ce ta farko tun bayan ballewar kasar Sudan ta kudu.