Faransa

Gwamnatin Faransa ta dauki matakan tsuke bakin aljihu

PM kasar Faransa François Fillon
PM kasar Faransa François Fillon REUTERS/Benoit Tessier

Gwamnatin kasar Faransa ta bayyana wasu sabbin matakan tsuke bakin aljihu da zasu sa gwamnatin ta yi tsimin makudan kudade bana.PM kasar Faransar Francois Fillon wanda ya gabatar da bayanan na nuna cewa an zabtare kashe kudaden da suka kai kudin Turai sama da Euro bilyon 12, da kuma kara yawan kudade haraji domin cike duk wani gibi.Fillon ya ce ala tilas ne su dauki matakan tada komadan tattalin arzikin kasar tasu domin ba za a dauwama ba a yadda ake.Ya ce kasar Faransa dole ta yi la'akari da harin da tattalin arzikin duniya ke ciki wajen daurewar ingancin nata tattalin arzikin.Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, ya sha nanata cewa tattalin arzikin kasar Faransa dai babu wani abin fargaba akai.Domin tabbatar da ana bin tsarin kashe kudade da aka shata, nan da badi waccan PM Fillon, ya ce za ayi karin haraji kan kudade shiga da ake samu da suka haura euro dubu 500 a shekara, sannan kuma za a kara harajin sigari, barasa, kayan zaki da makamantansu.