Najeria

Hukumar kare hakkin bil Adama ta koka da fadadan cin hanci na Nigeria

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Akintunde Akinleye

Hukumar kare hakkin bil Adama ta Duniya, Human Right Watch, ta bayyana cewa Hukumar yaki da cin hanci ta Tarayyar Nigeria, EFCC, wadda aka kafa cikin shekara ta 2002, ta gaza wajen gudanar da aiyukanta.Daraktar hukumar na Nahiyar Afrika, Daniel Bekele, ya ce akwai fata mai haya, lokacin da aka kafa hukumar bayan kawo karshen mulkin soja, saboda yakan cin hanci cikin kasa mafi yawan mutane cikin nahiyar ta Afrika.Hukumar ta yi nuni da yadda cin hanci da rashawa ke kara samun gindin zama, da kuma yadda ‘yan siyasa ke haddasa rikice rikicen siyasa, da yadda zaman takewar rayuwa ke lalacewa.